Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) sun yi watsi da sabon kiraye-kirayen a saki shugaban haramtacciyar kungiyar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu.

Kungiyar IPOB ce ke jagorantar fafutukar kafa kasar Biyafara mai cin gashin kanta.

Kakakin kungiyar, Abdul-Azeez Suleiman, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce kiraye-kirayen a saki Kanu ba tare da shari’a ba da shugabannin da kungiyoyin Ndigbo suka yi ya kara kamari tun bayan zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kungiyar ta Arewa ta yi nuni da cewa kungiyoyi irin su Ohanaeze Ndigbo sun shiga cikin yakin zagon kasa ta hanyar yin amfani da sakin Kanu a matsayin wani sharadi na hadin gwiwa da Ndigbo da gwamnatin Tinubu mai zuwa wanda ba su taba zabe ba kuma babu wata hanyar da za ta iya kai wa ga nasara.

Don haka kungiyar ta yi Alla-wadai da sabbin kiraye-kirayen a dakatar da shari’ar Kanu da kungiyar Ohanaeze da sauran shugabanni da kungiyoyi na Ndigbo suka yi, inda ta bayyana shi a matsayin rashin tunani, rashin sanin ya kamata, rashin tunani da rashin gaskiya.

Ta nanata kira ga hukumomin tarayya da su yi watsi da irin wadannan kiraye-kirayen na rashin kishin kasa, su kuma jajirce wajen ganin an gurfanar da Kanu a gaban shari’a don kada a kafa wani mummunan misali na yadda shugabannin yankin ke tsoma baki a shari’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: