Hukukar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC reshen jihar Kano ta sha alwashin gudanar da sahihin zaɓe yayin da za a kammala zaɓe a wasu kananan hukumomin jihar.

Kwamishinan zaɓe a jihar Ambasada Abdu Abdusdaamad Zango ne ya tabbatar daa haaka yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a helkwatar hukumar yau Laraba.

Za a kammala zabe a wasu rumfunan zabe na kananan hukumomi 16, daga ciki akwai kananan hukumomin Fagge da Tudun Wada da za a sake zaɓen wakilai a zauren majalisar tarayya.

Sai kananan hukumomi 14 da za a kammala zaɓen wakilai a zauren majalisar dokokin Kano.
Dukkanin su sun haɗa da rumfunan zabe guda 206 waɗanda galibi aka samu hayaniya da ta kai ga lalata kayan zabe.

Ya ce sun ɗauki darrusa da dama a sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna a jihar kuma za su tabbatar sun kiyaye faruwar haakan aa gaba.

Daga cikin manyan matsalolin da hukumar ta ce ta fuskanta akwai tayar da fitina a wajen kaɗa ƙuri’a wandaa hakan ya tayarwa da hukumar hankali.

Sai dai ya ce sun bibiyi dukkanin wuraren da aka samun tashin hankali tare da ɗaukar matakai domin ganin hakan ba ta sake faruwa ba.

Sannan ya buƙaci jam’iyyun siyasa da su kasance masu kwarin gwiwa a kan zaɓen da za a yi don ganin sun gudanar da zaɓen ba tare da wata matsala ba.

“In Allah ya yarda a ranar Asabar za a gudanar da kammala zabe, kuma za mu sanar da cikakken sakamako babu daɗi babu ragi, sannan duk wandaa ya ke ji bai gamsu da sakamakon ba zai iya daukar mataki da doka ta tanada”.

Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyyu, kungiyoyi masu zaman kansu, shugabannin addinai, jami’an tsaro, da wakilin sarkin Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: