Wani abun fashewa da ake kyautata zaton Bom ne ya fashe a garin Dutse babban birnin Jihar Jigawa.

 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar SP Lawan Shisu Adam ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Shisu ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:40 na daren ranar Talata akan titin Hakimi cikin garin Dutse hakan ya yi sanadiyyar jikkatar mutum guda.

 

Kakakin ya ce tuni jami’ansu su ka fara gudanar da bincike akan lamarin domin gano sanadiyyar fashewar abun.

 

Lawan Shisu Adam ya bukaci mazauna yankin da su gujewa shiga cinkoso ko kuma bayar da rahotan wani abu da ba su gamsu dashi ba.

 

Wani mai suna Friday Frayo da abin ya faru akan idansa ya bayyana cewa ya dauki wani abu a cikin bakar leda inda ya ga wata na’ura tana harbawa a ciki daga bisani ya jefar da ita.

 

Friday ya ce bayan jefar da ledar yayi na’urar ta tashi wanda hakan ya sanya ya samu raunika a jikinsa.

 

Ya ce babu wanda ya rasa ransa sai dai wani allon sanarwa da ya lalace a kusa da shagonsa.

 

Bayan Fashewar abin ya haifar da zaman dar-dar a zukatan mutanen garin na Dutse.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: