Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Jihar Kogi Alhaji Mukhtar Bajeh (APC Okehi) yayi murabus daga kan mukaminsa tare da maye gurbin sa nan take.

Dan Majalisar mai wakiltar Okehi a jam’iyyar APC ya dauki matakin hakan ne domin nuna adawa akan zargin da ake yi masa da hannu da laifin aikata ta’addanci tare da wasu abokansa Takwas.
Idan ba a manta ba dai a ranar 25 ga watan Maris gwamnan Jihar Yahya Bello ya bayyana wasu mutane tara daga cikin 25 na ‘yan majalisar dokokin a matsayin ‘yan ta’adda bayan zargin su da ake yi da aikata ta’addanci a ranar zaben gwamnonin Jihohin da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa murabus din na zuwa ne ta cikin wata wasika da gwamnan ya aikewa kakakin majalisar Matthew Kolawale.
gwamnan ya nemi da a dakatar da mutane tara ciki harda shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Jihar tare da gudanar da bincike akan su.

Bayan dakatarwar shugaban masu rinjayen ya aikewa majalisar wasikar sauka daga kan mukamin sa.
Kazalika bayan kammala karanto wasikar ta shugaban masu rinjayen kakakin majalisar yaji ta bakin sauran ‘yan majalisar ,inda su ka amince da nada Hon Ahmad Dahiru a matsayin sabon shugaban wanda a baya ya kasance mai ladabtarwa a majalisar.