Jami’an sojin Najeriya sun garƙame wasu gidajen masu zaman kansu na yara masu kananan shekaru da ke Kasuwar Fara a Rukunin gidajen Shagari Low-cost a garin Maiduguri da ke Jihar Borno.

Jami’an sun rufe gidajen ne bayan wani rahoto na musamman da Jaridar Daily Trust ta yi akan yadda ake aikata masha a a wadannan gidajen na masu zaman kansu.
Mazauna yankin sun bayyana cewa an kuma samu nasarar kama wasu mutane bayan jami’an sojin sun kai sumamen kwanaki biyu da su ka gabata.

Wata mazauniya a yankin mai Suna Halima Abdul ta bayyana cewa bayan kamun da jami’an sojin su ka yiwa mutanen ba a san idan su ka nufa da su ba.

Halima ta tabbatar da cewa bayan kama mutanen mazauna yankin sun shiga cikin kwanciyar hankali,bayan shafe tsawon shekaru ana cin zarafin su.
Shima wani mai suna Solomon Joseph ya yaba bisa kokarin da sojojin su ka yi tare da rokon su da su bar ‘yan kasuwar ta Fara da su ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancin su a yankin.