Gwamnatin tarayya ta amince da kashe kudi kimanin naira biliyan 250 a shirinta na rage radadin talauci a fadin kasar.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo shi ne ya bayyana haka a lokacin wani jawabi na cigaban da aka samu a shirin gwamantin tarayya na rage radadin talauci da ake kira NPRGS.
Ayyukan da aka tsara aiwatarwa a wannan shekara karkashin shirin na NPRGS sun hada da gina gidaje dubu dari ga masu karamin karfi, aikin da zai samar da ayyukan yi na kimanin mutane miliyan daya ga al’ummar kasar, baya ga fadada samar da makamashi ta hanyar samar da fitilun kan tituna 1,200 a yankunan karkara.

Kana ana sa ran shirin zai samar da naira biliyan 9 ga manoma masu karamin karfi a daminar bana karkashin shirin samar da ayyukanyi a fannin noma a fadin kasar, tare da samar da hanyoyi a yankunan karkara da zasu hada kasuwannin kauyuka 750 a fadin Najeriya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun maitaimakin shugaban kasa ya fitar a jiya alhamis sanarwar ta ce Kimanin Matasa 13,000 ne suka sami horo akan kere-kere da sana’o’in hannu a jihohi 6 na kasar da suka hada da Gombe, Legas, Kaduna, Ogun, Enugu da jihar Nasarawa, yayin da ake shirin samar da irin wannan tsari ga matasa 2,000 a jihar Edo.