Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Edo ta nemi karin kujeru 150 daga hukumar aikin Hajji ta kasa NAHCON domin bai wa maniyyatan jihar damar sauke farali.

Shugaban Hukumar Sheik Ibrahim Oyerekua shine ya bayyana hakan ga manema labarai, ya kuma kara da cewa hukumar za ta rufe karbar kudin aikin hajji na wannan shekarar daga ranar 21 ga wannan wata.

Ya ci gaba da cewa jihar ta sami kujeru 274 sai dai maniyyatan jihar sun kai 355 wanda yawancinsu sun biya kudadensu ga hukumar a cewarsa.

Sheik Ibrahim ya tabbatar da cewa sun mika bukatar karin kujerun ga hukumar Alhazai ta kasa a hukumance, wanda kuma hukumar ta yi al’kawarin duba bukatar tasu.

Kana ya shawararci wadanda basu kai ga kammala biyan kudadensu ba da su tabbatar sun biya kafin wa’adin da hukumar ta dauka ya cika.

Leave a Reply

%d bloggers like this: