Ɗalibai mata 2 na jami’ar tarayya da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, waɗanda suka shiga hannun masu garkuwa sun shaƙi isƙar ‘yanci.

 

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ɗaliban, Maryam da Zainab, sun kubuta daga hannun ‘yan bindiga bayan shafe kwanaki 12 a cikin Jeji.

 

Idan baku manta ba abaya an kawo rahoto cewa an sace daliban ne yayin da wasu yan bindiga suka kutsa gidan kwanansu a kauyen Sabon Gida.

 

Ƙungiyar ɗaliban jihar Zamfara ta tabbatar da dawowar daliban amma ba ta ce komai ba kan ko an biya kuɗin fansa kafin su kubuta.

 

Jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar, Umar Abubakar, ya taya shugabannin jami’a murna da kuma iyayen ɗaliban, waɗanda Allah kaɗai ya san halin da suka shiga bayan sace ‘ya’yansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: