Wasu da ake zaton mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram ne sun kai sabon hari a jihar Yobe, inda suka kashe akalla mutum tara.

 

Channels TV ta ruwaito cewa lamarin ya afku ne a ranar Alhamis, 13 ga watan Afrilu a Buni Gari, karamar hukumar Gujba da ke jihar.

 

Mazauna garin Buni Gari, Baba Ibrahim da Iliya Maina sun sanar da Channels TV cewa al’ummar yankin sun shiga tashin hankali ne lokacin da wani mutum mai suna Shettima Dawi ya tafi neman itattuwa a yan kilomita kadan da garin amma bai dawo ba.

 

 

Lamarin ya sa yan uwanda da makwabta haduwa don gano inda yake a cikin jeji, kawai sai mayakan Boko Haram suka farmake su.

 

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar yan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da harin.

 

DSP Abdulkarim, ya ce sabanin abun da rahotanni suka kawo, mutane tara yan ta’addan suka kashe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: