Akalla mutane 79 ne suka rasa rayukansu bayan kamuwa da cutar Amai da gudawa a Najeriya.

Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa NCDC ta kasa ita ce ta bayyana haka a jiya Litinin cikin wani sabon rahotanta da ta sake yi akan abun da ya shafi Amai gudawa.

NCDC ta ce an samu wadanda suke dauke da cutar a kasa Najeriya mutane 1336 cikin wannan shekarar da muke ciki.

Sannan adadin ya fito ne daga jihohi 13 na kasar dai dai da kananan hukumomi 43 a fadin Najeriya.

Jihohin dai sun hada da Jihar Abia, Bauchi, Bayelsa, Cross Riva, Ibonyi, kano da kma jihar Katsina.

Sauran sun hada da Niger, Ondo, Osun, Sokoto, da jihar Zamafara.

Sannan cutar tana kama yan shekaru 15 da 24 da kuma 45 kuma mafi yawa daga ciki mata ne da kaso 53 cikin dari sai maza 47 cikin dari.

Kamar yadda yake a rahotan hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce kasashe 24 ne ke fama da Amai da gudawa a duniya.

Ko a wani rahoto da aka fitar daga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya bayyana yadda ita kanta cutar ta Amai da gudawa take shiga jikin mutum.

Masanan su ka ce ita dai wannan cutar ta Amai da gudawa ana samunta ta hanyar amfani da ruwa wanda bai tsafta da kuma irin abincin da ya lalace kuma aka yi amfani da shi.

Sai dai daga karshe hukumar dakile cuta ta kasa NCDC ta ce za ta ci gaba da aiki da kwararru daga kowanne fanni domin ganin bayan cutar Amai da gudawa a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: