Babban kwamitin dubban watan musulunci a Najeriya karkashin mai alfarma sarkin musulmi Alhaji sa’ad ya bayyana cewa ranar Alhamis ita ce ranar da za a yi dubban jinjirin watan Shawwal.

Sanarwan hakan ta fito daga mai magana da yawun kwamiti harkokin addinin musuluncii na kasa karkashin sarkin musulmi wato Zubairu haruna Usman.

Ya ce kamar yadda yake a kowanne lokaci sun aikewa dukkanin wakilansu na kasa bakidaya domin sanarda ganin watan wanda yake bisa yadda dokar musulunci ta tanada.

ya ci gaba da cewa in Allah ya kaimu ranar Allhamis 29 ga watan ramadan zai zama ranar da za a fara dubban watan sallah.

Idan kuma bai ganu ba a ranar sai a jira zuwa ranar Asabar wadda ita ce zata zama ranar sallah kamar yadda kowa ya sani.

Sannan sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya sake jan hankalin mutane game yadda mahimmanci zakkar fidda kai ta ke, kuma ko menene ya shigewa alumma duhu sai su tambayi malamai domin karin bayani akan haka.

Daga karshe sarkin ya roki mutanen kasar da su sanya kasa Najeriya a cikin adduoin su cikin wannan goman karshe domin samun tsaro ga kasa da sauran abuwan sa suka zama koma baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: