Rundunar yan sanda a jihar Delta ta kori wani jamin ɗan sanda bayan hallaka wani ɗan kasuwa a kan hanashi cin hancin naira 100.

An kori Ubi Ebri mai muƙamin Isfekta bayan hallaka wani ɗan kasuwa mai suna Onyeka Ibe.
Alamarin ya faru a ranar 5 ga watan Afrilun da mu ke ciki a kan hanyar Ugbolu zuwa Illah a Asaba babban birnin jihar.

Yan sanda jihar sunsamu tabbacin mutuwarsa ne bayan kaishi babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Asaba.

Mai Magana da yawun yan sandan jihar ya tabbatar da korar jami’in a jiya Talata.
A sanarwar da kakakin yan sandan jihar ya fitar a jiya Talata, yace za su gurfanar da jami’in a gaban kotu a yau Laraba domin fuskantar tuhuma.