Rundunar ‘yan sanda ta gargaɗi dukkan masu aikata muggan laifuka, da ke shirin kulla makircin da ta da zaune tsaye lokacin ko bayan karamar Sallah su canja tunani ko su fuskanci fushin doka.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma sanar da kama ‘yan daban siyasa 26 a sassan jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.


Duk wannan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Ahmed Wakil, ya fitar ranar Talata a Bauchi.
Ya shawarci duk masu niyyar aikata muggan laifuka da ka iya kawo tasgaro ga zaman lafiya su tattara su bar jihar Bauchi domin babu wata ƙofar ɗa zasu aikata mummunan nufinsu.
SP Wakil ya tabbatar da cewa nauyin da ke kan yan sanda na kare dukiya da kadarorin mazauna Bauchi, tabbatar da bin doka da oda da sauransu, kuma sun shirya tsaf.
Kakakin ‘yan sandan ya ƙara da cewa hukumar zata ci gaba da zaƙulo duk wasu masu mugun nufi iyakar iyawarta kuma duk inda suka shiga zasu tabbatar sun shiga hannu.