Rigima ta barke tsakanin wasu Hausawa da Gwarawa da ke tuka Keke Napep, abin ya faru ne da safiyar yau Litinin a garin Abuja.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa rikicin ya barke ne a yankin 3rd Avenue da ke Unguwar Gwarinpa a babban birnin tarayya.


Bidiyoyi na yawo a kafofin sada zumunta da ke nuna wasu sun samu rauni.
Jaridar ta ce wani daga cikin mazauna Gwarinpa ya shaida mata sabanin tsakanin Hausawa ne da Gwarawa da ake ganin su ne ‘yan gari.
Majiyar ta ce lamarin ya kai mutane sun gagara fita waje saboda gudun an yi masu lahani, baya ga haka akwai wadanda suka samu rauni.
An yi kokarin tuntubar Kakakin ‘yan sandan reshen Abuja, SP Josephine Adeh, amma ba a dace ba, jami’an tsaron ba su amsa waya ba.