Daliban Najeriya da suka makale a kasar Sudan bayan barkewar yaki sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta taimaka ta gaggauta kwashe su.

A bidiyon wata daga cikin daliban mai suna Fauziyya, ta ce daga barkewar yakin, wanda ya yi kamari a birnin Khartoum ranar Karamar Sallah, kasashe da dama sun kwashe dalibansu daga Sudan, amma daliban Najeriya na cikin halin rashin tabbas.


A bidiyon Fauziyya wanda ya karade kafofin sada zumunta, ta ce hatta daliban kasar Malawi da ba su da ofishin jakadanci a Sudan an zo an dauke su, sai su kadai a Khartoum… kowa ya gudu ya bar su.
Tuni dai kasashen duniya ke ta janye jami’an jakadancinsu daga Khartoum, bayan kazancewan rikicin shugabancin na Sudan, wanda ya yi ajalin akalla mutum 200, baya ga wadanda aka jikkata da wadanda aka raba da gidajensu.
Fauziyya, wadda ta ce kudi da ruwan sha da abincin wasu daga cikinsu ya kare, ta kara da cewa kafin wayewar garin Lahadi an fara katse layukan sadarwa a sassan Khartoum.
Ta ce, katse layukan sadarwar na iya sa, Ko an zo daukar su ba za a same su ba.
Sun bayyana mata cewa daren wuta ta dauke, ba su da abinci, ba su da ruwa.
Fauziyya, wadda ta ce kudi da ruwan sha da abincin wasu daga cikinsu ya kare, ta kara da cewa kafin wayewar garin Lahadi an fara katse katse layukan sadarwa a sassan Khartoum.
Don haka ta yi roko da a yi duk abin da za a yi domin a kwaso su zuwa gida kamar yadda sauran kasashe suka yi wa dalibansu.
Wannan bayani na Fauziya, ba zai rasa nasaba da bayanin Gwamnatin Tarayya cewa kwaso daliban da suka kamale a Sudan zai yi wuya a halin rikicin da ake ciki ba, amma gwamnatin ta kafa kwamitin kwaso su.
Sai dai a ranar Lahadi, kungiyar Daliban Najeriya da ke Sudan ta fitar da wata sanarwa da ke kira gare su da su hadu a Jami’ar Ifriqiyya ko Jami’ar El-razi ko ofishin kungiyar, domin a kwashe su zuwa kasar Habasha.
Kazalika, Shugaba Buhari ya bukaci daliban da suka makale su kwantar da hankalinsu, su kuma zauna cikin gida, yayin da gwamnati ke kokarin turawa a kwaso su.
- Buhari ta hannun kakakinsa, Garba Shehu, ta ce, tana aiki haikan da ofisoshin jakadancin kasashen Sudan da Habasha, domin ganin an kwaso daliban cikin aminci.