Gwamnonin Najeriya 36 za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tattaunawa da shi game da samar da sabuwar hanyar samar da kudaden shiga tare da mika wa majalisa ta 9 kafin karewar gwamnatinsa.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar gwamnonin a jiya Laraba 26 ga Afrilu.
Tambuwal ya ce, gwamnonin sun tattauna da Buhari game da lamuran da suka shafi kasa, dimokradiyya da shugabanci nagari, ciki har da batun da ya shafi CBN da kudaden haraji.

A jawabin sa ya ce a yau sun tattauna ka’idojin da Hukumar Leken Asirin Kudi ta Kasa (NFIU) ta fitar kan ka’idojin kudi da take aiki a kai wajen ganin an fitar da Najeriya daga jerin sunayen masu ba da harajin kudi.

Sun kuma tattauna batun ayyana samar da kananan asibitoci da ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu.
A yayin bitarsu, wasu jahohin da suka samu wasu nasarori za su sami wasu kyautuka saboda kwazon da suka yi.