Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana cewa bayan mika mulki ga zababban shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu zai zauna a mahaifarsa Daura ne Kawai na tsawon watanni Shida.

 

Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa malam Garba Shehu Jim kadan bayan kammala ganawa da gwamnonin jam’iyyar APC a ranar Alhamis a fadarsa da ke Abuja.

 

Buhari ya ce bayan ya kammala zaman watanni shida a garin Daura dake Jihar Katsina zai koma Jihar Kaduna ne da zama.

 

Gwamnonin karkashin jagorancin Atiku Bagudu gwamna Jihar Kebbi sun kaiwa shugaban ziyarar ne domin tayashi murnar lashe zaben da jam’iyyar su ta APC ta yi a zaben da aka gudanar.

 

Ziyarar ta samu halartar gwamnonin Jihohin Jigawa Kaduna Filato Ekiti Imo Kwara Nasarawa Cross Rivers Katsina Ogun da kuma Legas.

 

Gamnonin Jihohin Kano Gombe Borno da Kumar Ebonyi sun aike da wakilcin mataimakan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: