Jamiyar mai jiran gado ta NNPP ta bayyana cewa gwamnatin jihar kano mai barin gado tana yin wani shiri da bai dace ba wajen shirin mika mulkin a ranar 29 ga watan Mayu mai kamawa.

Wannan ya fito ne daga bakin shugaban kwamitin karbar mulki na jamiyar NNPP na jihar kano wato Abdullahi Baffa Bichi a wani taro da yayi da yan jaridu a jiya Juma a .
Baffa Bichi ya ce jamiyar APC ta na yin wani shiri na yin zagon kasa a mika mulkin.

Ya ce a ka’ida ba mai bayar da mulki ne zai kawo kaso 82 na mika mulki ba, don kuwa hakan ya sabawa dokar.

Ya ce yan jihar za su iya yarda da tsarin karbar mulki kamar yadda yake a doka suma na jamiyar NNPP kaso uku ne.
Sai dai a wani rahoto da yake ishemu yanzu ta hannun kwamishinan yada labarai Mahammad Garba ya ce gwamnati mai barin gado bata yin wani shiri na zagon kasa game da mika mulki.
ya ce wannan bayanan da jamiayar NNPP ta ce ana yin zagon kasa ba tabbatacce ba ne kuma gwamnati ta shirya duk wasu takardu domin tabbatar da ta bayar da mulki a ranar 29 ga watan mayu.
Tun bayan hambarar da gwamnatin APC a kano aka dinga musayar maganganu inda shi kansa mai ci gwamna tare da sukar juna.