Rundunar yan sanda Najeriya reshen jihar Anambara ta tabbatar da kama wasu mutane Uku da take zargi yan awaren kasar Biyafara ne.

kwamishinan yan sandan jihar Echeng Echeng shi ne ya bayyana haka ga manema labarai.
Echeng ya ce wadanda ake zargin an kama su a ranar Laraban data gabata tare muggan kayan laifi.

Kayan wadanda da suka hada da bindigu kirar AK 47 da kuma harsashi masu yawa sai kayan yan sanda na bogi a jikinsu da kuma babbar mota kirar Toyota.

Ya ci gaba da cewa dukkaninsu ba yan jihar Anambara ba ne wato akwai dan Abiya da Osun da kuma Enugu.
Sannan ya ce za a ci gaba da bincike kamar yadda yake kafin daga bisani a kaisu izuwa kotu domin yanke hukunci.