Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce ba su kirkiri karin masarautu a jihar domin a rushesu ba.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron da aka shirya a Kano don taya murnar zagayowar ranar ma’aikata ta duniya.
Hakan na nuni da martani ga tsohon

gwamnan Kano Sanata Rabi’u Kwankwaso wanda ya yi magana a kan batun.

Wani faifan bidiyo ya yi ta yawo wanda aka hango Sanata Kwankwaso na bayyana cewar sabuwar gwamnati karkashin jam’iyyar NNPP za ta duba tsarin masarautun bayan sun karɓi mulki.
Sai dai gwamna Ganduje ya ce samar da tsarin sabbin masarautun a jihar alama ce ta
haɗin kai da cigaba.
Tsagen gwamnati mai ci da gwamnati mai jiran gado na jifan juna da kalaman zargi tun bayan ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna da aka yi a watan Marin ɗin da ya gabata.