Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja zuwa birnin Landan na kasar Birtaniya yau Laraba, domin halartar taron da aka gayyace shi na bikin nadin sarautar sarki Charles na uku.

Za a yi bikin nadin sarki Charles na uku da matarsa Camilla a matsayin sarki da kuma matar sarki sarauniya na yankin tarayyar Birtaniya baki daya.
Mai bai wa Shugaba Buhari shawara na musamman a fannin yada labarai da Hulda da jama’a Femi Adesina, shi ne ya bayyana batun bulaguron shugaban a yau Laraba.

Ya kuma bayyana cewa yayin bikin nadin, kungiyar kasashe rainon Birtaniyan zasu yi taron ganawa na shugabannin kasashensu a ranar Juma’a 5 ga watan Mayu.

Ya kuma kara da cewa Buhari zai himmatu ga halartar taron, Wanda zai mayar da hankali ga cigaban kasashe rainon Birtaniya da kuma rawar da matasa zasu taka.
Shugabannin na kasashen rainon Birtaniya zasu gudanar da taron ranar Juma’a, washegari kuma ranar Asabar a gudanar da bikin nadin sarki Charles na uku.