A yayin da ya rage Kasa da kwanaki a 23 a rantsar da sabon shugaban Kasar Najeriya Bola Tinubu an fara yiwa fadar shugaban Kasa Kwaskwarima domin samar da kyakkyawan yanayi.

 

Gabanin rantsar da sabon shugaban Kasar Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayun da muke ciki aka dauki matakin gyaran.

 

Mai magana da yawun shugaba Buhari Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a shafinsa na sa da zumunta.

 

Garba Shehu ya ce masu Fenti da sauran masu aiki tuni su ka fara aiki domin ganin ta yi kyawun gani ga sabon shugaban.

 

Shehu ya kara da cewa an dauki kwararrun ma’aikata domin su gudanar da gyaran a fadar ta shugaban Kasar.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: