Gwaman Jihar Ebonyi kuma zaɓaɓɓen Samara Dave Umahi ya bayyana janyewa daga kudurinsa na zama shugaban Majalisar Dattawa.

Umahi ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a Jim kadan bayan kammala ganawa da sabon shugaban Kasa Bola Tinubu, inda ya bayyana janyewa daga neman zama shugaban Majalisar ta dattawa.


Jaridar The Cable ta ruwaito cewa gwamna Umahi ya janye daga neman takarar ne domin goyon bayan tsohon gwamnan Akwa Ibom Godwill Akpabio.
Dave ya ce ya gana da Tinubu inda kuma ya bashi umarnin ya janye daga takarar.
Umahi ya kara da cewa ko da takarar mataimakin shugaban majalisar ba zai shiga ba.
A nasa bangaren Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu Ali Ndume ya shaidawa manema labarai cewa Akpabio shine dan takarar da aka tsayar a yayin taron.