Akalla mutane Takwas ne su ka mutu ciki har da wata da ta ke shirin amarcewa a jihar Zamfara.

Mutanen sun mutu ne sakamakon kifewar wani kwale-kwale a Gusau babban birnin jihar yayin da su ke tafiya don neman ruwna da za su sha.
Lamarin ya faru a ranar Lahadi.

Wani mai suna Halilu mazaunin unguwar Bugaje a Gusau, ya bayyana a tattaunawarsu da BBC cewar, ruwan ana amfani da shi ne kadai wajen wanki.

Ya ce wasu mutane na amfani da kwale-kwale wajen ketara ruwan zuwa wajen da wasu su ka gina rijiya don nemo ruwan sha.
Ya ce daga ciki akwai wata da ake daf da daura mata aure wanda tuni aka kammala shirye-shirye.
Rahotanni sun ce wasu yankuna a Gusau ana fama da karancin ruwan sha wanda mutane ke tafiya mai nisa domin nemo ruwan da za su sha.