Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci amincewar majalisar dattawan kasar na ranto bashin dala miliyan 800.

Bashin da shugaban zai karbo daga bankin duniya.

A wata wasika da shugaban ya aikewa majalisar ranar Laraba wanda shugaban kajalisar Ahmad Lawal ya karanta.

Sabon bashin da shugaban ya bukaci rantowa, za a yi amfai da su ne wajen tallafawa yan ƙasar da ke fama da talauci.

Ya bukaci amincewsr haka daga majalisa don ganin an cika muradin.

Wasikar ta ce za a aika kuɗaɗen zuwa ga yan kasar kai tsaye ta asusun ajiyarsu na banki kai tsaye.

Buƙatar karbo bashin an karanta a majalisa ne yayin da ya rage ƙasa da wata guda shugaba Buhari ya yi adabo da mulkin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: