Rundunar ‘yan sandan Jihar Oyo ta tabbatar da kama wasu mutane uku wadanda su ka bayyana mata cewa su ne suka hallaka wani Mataimakin Sufurtandan ‘yan sanda ASP Ogunleye Olufemi Daniel a unguwar Ori-Agogo a yankin Odo-Ona Kekere a garin Ibadan na Jihar Oyo.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar SP Adewale Osifeso shine ya bayyana hakan a yayin holansu ga ‘yan Jaridu a ranar Juma’a a garin Ibadan.


Kakakin ya ce mutanen da aka kama sun hada da mai shekaru 80 da mai shekaru 25 da kuma 26,inda su ka bayyana wa rundunar cewa sun hallaka dan sandan ne a harin da su ka kai unguwar a karshen watan Afrilu.
SP Adewale ya ce Mataimakin Sufeton Ogunleye yana aiki ne a sashin binciken manyan laifuka na CID a lokacin da su Ka kai harin unguwar ta Ori-Agogo inda ya ke zaune tare da iyalansa.
Kakakin ya kara da cewa bayan hallaka Ogunleye sashin binciken manyan laifuka ya fara aikin binciko wadanda su ka hallaka shi wanda hakan ya kai ga an samu nasarar kama mutanen.
SP Adewale ya bayyana cewa an samu wayoyin hannu da mota da karamar bindiga da aka samu a hannun su wadanda su ka kasance mallakar marigayin ne.
Sannan Kakakin ya ce an kama mutanen tare da wata mata mai suna Iya-Alaye wadda take sayan sarkokin wuya na gwala-gwalai a hannun mutanen bayan sun sato.