Rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara ta bayyana Kama wani likita mai suna Dr Ayodele Joseph wanda ake zarginsa da yiwa wata mara lafiya Fyade a Asibiti.

A yayin holan Wanda ake zargi a ranar Juma’a Kwamishinan ‘yan sandan Jihar ya ce Paul Odama, ya bayyana cewa sun gurfanar da shi ne sakamakon saba dokar tsare mutane da yayi..


Kwamishinan ya bayyana cewa jami’an sun kama wanda ake zargi ne a ranar Laraba bayan binciken da su ka gudanar a kansa.
Odama ya kara da Cewa a baya ma an taba gurfanar da likitan a gaban Kotu bisa sanadiyyar rasa ran wani mutum mai suna Nneka Akanike a Asibitin sa.
Kwamishinan ya ce sun gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu domin yi masa hukunci akan aikata laifin fyade da yayi.