Shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, ya umarci kafatanin Ministocinsa su ci gaba da ayyukan Ofisoshinsu har zuwa ranar ƙarshe da wa’adin gwamnatinsa zai ƙare.

 

Jaridar Daily Trust ruwaito cewa shugaba Buhari zai miƙa ragamar mulkin Najeriya ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, 2023.

 

 

Shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, ya ƙara bayani kan shirye-shiryensa na ritaya bayan sauka daga kujerar mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

 

Buhari ya yi ƙarin haske kan shirinsa ne a wurin kaddamar da katafariyar Hedkwatar kwastam ta ƙasa a birnin tarayya Abuja ranar Talata, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

 

 

Wata motar bas dauke da mahajjata daga jihar Nasarawa zuwa Abuja don tafiya kasa mai tsarki ta yi hatsari.

 

Manema labarai sun ruwaito cewa motar bas din mai dauke da wurin zama 18 ta yi hatsarin ne a kusa da Kara a karamar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa a ranar Laraba 24 ga watan Mayu.

 

 

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da mataimakinsa sun yi ja in ja a bainar jama’a yayin zaman majalisa a ranar Laraba, 24 ga watan Mayu kan wata sanarwa da shugaban majalisar ya yi game da takardar umarni na ranar Alhamis.

 

Gbajabiamila dai ya bukaci a takaita takardar domin ba yan majalisar damar halartan taron kaddamar da Cibiyar Nazarin Dimokradiyya da Dokoki ta kasa (NILDS).

 

 

Babban bankin Najeriya (CBN) ya kara kudin ruwa zuwa kashi 18.5 cikin dari don dakile hauhawan farashin kayayyaki.

 

A makon da ya gabata, tashin farashin kayayyaki a kasar ya haura zuwa kashi 22.22 musamman hauhawan farashin kayan abinci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: