Rundanar yan sandan kasa Najeriya ta kammala bayar da horon kwanaki Uku da ta shiryawa jami’anta a babban brinin tarayyar Abuja.

Mai gana da yawun hukumar yan sanda ta kasa Olumuyiwa Adejobi shi ne ya bayyana haka a dandalin facebook a yau Alhamis.
Adejobi ya ce hukumar ta bayar da horon ne na tsawon kwanaki Uku sakamakon yadda hukumar za ta kara tunkarar lamarin tsaro a kasar.

Hukumar ta bai wa bangare daban daban da suka hada matakai da na ko ina a bangaren hukumar yan sanda.

Sannan ya ce akwai wasu jami’ai da aka yiwa karin girma zuwa matakin daban-daban wadanda ke bayar da kariya ga masu ruwa da tsaki aka bai wa horon.
Taron wanda aka gudanar a babbar Helkwatar tsaro ta yan sanda a babban birnin Najeriya.