Kwamitin aikin hajji a jihar Bauchi ya buƙaci masu ruwa da tsaki da su tabbatar sun samar da kyakkayawan yanayi ga maniyyata aikin hajjin bana na shekarar 2023.

Shugaban kwamitin kuma sarkin Ningi Alhaji Yunus Muhammad Sanyaya ne ya bukaci haka yayin ganawa da maniyyata aikin hajji.
Ganawar da aka yi a maniyyata da masu ruwa da tsaki a hukumar jin daɗin alhazai ta Sultan Sa’ad Abubakar a jihar.

Shugaban kwamitin y ace kula da maniyyata tare da sauke nauyin da ke wuyansu abu ne da ya dace a haɗa hannu domin kammala aikin.

Sannan ya buƙaci masu ruw ada tsaki da su ƙara ruɓanya koƙarinsu don ganin sun sauke nauyin da ke wuyansu na maniyyatan.
Sannan ya gargadi masu kula da maniyyata a jihar da su kasance cikin kayan da aka ware musu a kasar saudiyya wanda hakan zai saukaƙawa maniyyatan gane jagororinsu a can.
Shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Danlami Ahmad Kawule, y ace wajibi ne su tabbatar sun kula tare da sauke nauyin da aka ɗora a kansu.