Rantsatstsen gwamnan jihar Katsina Dikko Radda ya lashi takobin magance matsalar ƴan bindiga da ta addabi jihar.

Sabon gwamnan ya bayyana haka ne a cikin jawabinsa da yay i bayan rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar Katsina.

Sannan y ace zai tabbatar gwamnatinsa ta yi wani abu na jin ƙai ga mutanen da hare-haren ƴan bindiga ya shafa a jihar don rage musu raɗaɗin abin da ya shafe su.

Haka kuma gwamnatin za ta sanya buƙatun mutane a gaba tare da ganin an biya musu.

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar ta yi tsarin bayanann asusun ajiya na banki guda ɗaya don tantance masu amfani da asusun banki.

Sannan ya bukaci shawarar shugabannin gargajiya a kan tsarin mulkinsa tare da ƙarfafarsu a kan haka.

Sabon gwamnan Katsina ya sha rantsuwar fara aiki a yau Litinin wanda sarkin Katsina Dakta Abdulmuminu Kabir Usman ya halarta tare da sauran manyan baƙi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: