Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Daura mahaifarsa bayan kammala taron rantsar da sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.

Muhammadu Buhari ya samu tarba daga sabon gwamnan Katsina Dikko Radda da mutanen Daura bayan sauka a yau Litinin.

Mutane da ɗalibai yan makaranta sun tarbi shugaban tare da rera waƙar Oyoyo Baba bisa rakiyar jami’an tsaro.

Tun kafin wannan rana tsohon shugaban ya bayyana cewar ya ƙagu ya sauka daga kujerar shugaban kasa tare da miƙata zuwa ga zaɓaɓɓen shugaba.

Tsohon shugaban ya ce ya fuskanci matsin lamba musamman yayin da yak e gab da kammala wa’adinsa na biyu.

Muhammadu Buhari ya shugabanci Najeriya tsawon shekara takwar wanda ya fara daga shekarar 2015.

Daga cikin ayyukan da shugaban ya lashi takobin yi har da magance matsalar tsaro da farfaɗo da fannin noma, samar da aikin yi da bunkasa tattalin arziƙi har ma da yaƙi da cin hanci da rashawa.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: