A yau Talata ne aka wayi gari da matsanancin wahalar mai wanda ake yi tsawon layin Dogo kafin samun fetur a mafi yawan fadin kasar Najeriya

A jiya ne Litinin aka 29 ga ga watan Biyar aka rantsar da sabon shugabankasa da mataimakinsa da gwamnoni wandanda aka zaba.
Amma dai wahalar man fetur din na da alaka da cire tallafin man da shugaban Najeriya Bola Tunubu ya ayyana a lokacin rantsuwarsa.

Da yake bayani Bola Tunubi a babban birnin tarayyar Abuja bayan karbar rantsuwar kama aiki ya ce ya cire tallafiin man fetur wanda ake hallaka makudan kudade kuma yan kasa ba sa karuwa ciki.

Sai dai shima babban kamfanin dallacin mai na kasa NNPC ya bayyana cewa ya ji matukar jin dadi bisa cire wannan tallafin.
Cikin bayanan da kamfanin ya fitar ya ce cire tallafin zai sanya a yi wasu abubuwan na morawa kasa da kudaden.
Yayin da wasu daga cikin mutane ke kara jin dadi bisa wannan da kuma akasi haka.
wasu da cikin mutane na kokawa a dangane da wahaar mai wadda galibi wasu gidajen mai su ka kasance a rufe.