hukumar yan sandan farin kaya ta DSS sun yi dirar mikiya a ofishin hukumar dakile masu yiwa tattalin arzikimn kasa ta’anati wato EFCC ta jihar Legas.

Kamar yadda kafofin yada labarai na kasar suka dinga rawaitowa sun bayayana yadda DSS suka hana ma’aikatan EFCC shiga ofishin.
Jaridar Punch ta rawaito daga wani ma’akacin hukumar ta EFCC dan nufin cewa a boye sunansa ya ce asalin wajen na hukumar DSS ne amma kuma EFCC dake Ikoyi ya ke yin amfani da shi.

Jami’in ya ci gaba da cewa batu ne tsakanin hukumomi biyu sai dai har yanzu ba a je gaban shari a ba amma kafin yau basu taba yin wata takaddama ba.

To amma yanzu ba su san manene ya sa suka je har 20 suna neman hanasu shiga ofishin ba.
Sai dai mu na tsaka da tattara wannan labari ne kwatsam sai ga sanarwa daga hukumar ta DSS kan cewa ba a hanasu shiga ofishi ba hasalima babu takaddama da ta faru tsakaninsu da hukumar EFCC.