Hukumomin tsaro a jihar Imo sun tabbatar da kubutar da karin mutane uku daga hannun yan garkuwa da mutane.

kamar yadda Dauda Aliya shugaban karamar hukumar ta Koto ta jihar Imo ya bayyana a jiya Litiinin.

wasu da ake zargin yan bindiga ne sun yi garkuwa da akalla mutane da dama akan babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja.

Ya ce jami’an tsaro hadi da Sojoji da yan sanda da kuma yan ciivil defence da yan bijianti sun samu damar kubutar da mutane uku ciki harda mai wata mata dauke juna biyu.

Shi ma a nasa bangaren mai bai wa gwamna shawara Jerry Omodere ya bayyana nasarar da jami’an su ka samu a yayin sumamen bayan kubutar da mutanen da aka sace.

Ya ci gaba da cewa akalla mutane Goma ne suka samu damar shakar iskar yanci daga wajen yan bindigar a baya.

Daga karshe ya ce gwamnatiin jihar Imo ta na mai yabawa jamian bisa irin wannan namijin kokari da kuma kira da su ci gaba da rubanya kokarinsu.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: