Tsohon shugaban kasa Mahammadu Buhari ya bayyana cewa shanunsa na garin Daura sunfi yan Najeriya saukin kai.

Buhari ya bayyana cewa shanunsa a matsayin wadanda suka fi yan Najeriya saukin juyawa.
Buhari ya bayyana haka ne a ranar Lahadi lokacin da aka shirya wata liyafar cin abinci da kuma mikawa shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu shaida a matsayin shugaban kasa.

Inda ya ce shanunsa na daura sune wadanda ke da saukin sarrafawa fiye da mutanen kasar tunda duk inda ka umarce su za su bi da kuma yin hakuri da abin da aka yi musu.

Ya ci gaba da cewa ya kagu gari ya waye domin ya mika mulki ga Tunubu inda zai kama hanyarsa ta zuwa Daura jihar Katsina wajen shanunsa masu saukin sarrafawa.
sannan daga karshe Buhari ya ce yana mai neman afuwar yan kasar bayan wasu abubuwa da suka faru a mulkinsa.
Daga karshe yana mai yabawa shuwagabanin kasashe kamar na kasar Afrika ta kudu na Ghana da Saludo