Kotun Masana’antu ta kasa da ke jihar Kano ta ba da umarnin a maida Muhuyi Magaji Rimingado a matsayin shugaban Hukumar Yaki da Rashawa (PCACC) ta jihar Kano ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnatin jihar Kano da majalisar jihar ne suka shigar da karar Muhuyi da neman kotun da sauke shi daga matsayinsa.
Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Ebeye David Eseimo ya ce ba a yi wa wanda ke karar adalci a sauraran karar ba kuma majalisar jihar ba ta da hurumin korarshi a matsayin sa.

Ya kara da cewa majalisar ba ta da wannan karfin iko ba tare da yin adalci ga kowane bangare a sauraron karar ba.

Mai Shari’an ya ce an sallami Muhuyi daga mukaminsa ta hanyar da bata dace ba, don haka kotun ta ba da umarnin mayar da shi mukaminsa ba tare da bata lokaci ba.
Jaridar Daily Trust ruwaito cewa an dakatar da Muhuyi daga mukaminsa, kafin daga baya tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar ya sallame shi gaba daya a mukamin nasa.
Tsohon gwamna Ganduje ya cire shi ne a mukamin nasa bayan da majalisar jihar ta bankado cewa akwai zarge-zarge da korafi da dama da ake tuhumarsa akansu.
Muhuyi a nasa bangaren, ya fada wa ‘yan jaridu cewa tsohuwar gwamnatin Ganduje ta cire shi ne a mukaminsa saboda yana binciken wata badakala ta manyan ayyuka da ya shafi iyalan gwamnan.