Gwamnan jihaar Kebbi Nasir Idris, ya bukaci maniyyata aikin hajjin bana daga jihar da su kasance jakadu nagari a tsawon zaman da za su yi a kasar Saudiyya yayin da suke gabatar da aikin hajjin bana.

Dakta Nasir Idris, ya bayar da wannan shawarar ne a lokacin da ya kai ziyarar bankwana da rukunin farko na maniyyata a sansanin alhazai da ke Birnin Kebbi, ya bayyana cewa, an san alhazan jihar da zama masu bin doka da oda, inda ya yi kira gare su da su kiyaye irin wannan dabi’a.

Gwamna Nasir Idris, ya bukaci maniyyata aikin hajjin bana daga jihar Kebbi da su kasance jakadu nagari a tsawon zaman da za su yi a kasar Saudiyya yayin da suke gabatar da ibadar aikin hajjin bana.

Dakta Nasir Idris, ya bayar da wannan shawarar ne a lokacin da ya kai ziyarar bankwana ga rukunin farko na maniyyata a sansanin alhazai da ke Birnin Kebbi, ya bayyana cewa, an san alhazan jihar da zama masu bin doka da oda, inda ya yi kira gare su da su kiyaye irin wannan dabi’a.

Ya sanar da su cewa wannan shi ne karon farko da gwamnati mai ci ta shirya tsarin gudanar da aikin Hajji kuma ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin an gudanar da aikin jigilar mahajjata a filin jirgin sama na Sir Ahamadu da ke Birnin Kebbi amma hukumar ta aiyana cewa jirgin zai tashi ne a filin jirgin sama na Sakkwato.

Ya shawarci alhazai da su dauki irin wannan ci gaban a matsayin wani aiki na Allah inda ya ce shi ma zai yi aikin Hajjin bana tare da su don ba shi damar duba wuraren da ake bukatar gyara.

Gwamnan ya ba da tabbacin cewa an kammala duk wani shiri na jin dadin alhazai a kasar Saudiyya, sai dai ana jiran isowarsu kasa mai tsarki.

Haka kuma ya bukaci mahajjatan da su kara himma wajen yi wa shugabannin kasa addu’ar samun nasara tare da samun zaman lafiya da ci gaba a Najeriya.

A nasa jawabin, Amirul Hajj na jihar Kebbi na bana, tsohon ministan harkokin cikin gida, Janar Muhammadu Magoro mai ritaya ya shaida wa gwamnan cewa an samar da komai domin ganin an gudanar da aikin Hajji cikin sauki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: