Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar II, ya bayyana cewa akalla litattafai miliyan 3.2 daga ayyukan Malaman Addinin Musulunci 200 na Daular Usmaniyya ne aka gyara tare da buga su don rarraba su a fadin kasar nan.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro na kwanaki uku kan koyar da Addinin Musulunci a Afirka wanda ya gudana a dakin taro na Arewa House da ke Jihar Kaduna a ranar Talata.
Taron ya samu hadin gwiwar kungiyar hadin kan kasashen musulmi (OIC) da cibiyar bincike kan al’adun Musulunci da tarihin

Musulunci (IRCICA) Turkiyya da kuma Al Istiqama suka shirya.

Sultan Abubakar, ya ce an buga littattafan a cikin harsunan Ingilishi da Larabci da Hausa.
Ya bayyana cewa, baje kolin kayayyakin tarihi na Afirka zai taimaka wajen dawo da martabar ‘yan Afirka da kimarsu a nan gaba.
Shugaban taron, Farfesa a ɓangaren tarihi kuma tsohon mataimakin shugaban Jami’ar Jihar Adamawa, Farfesa Al Kasum Abba ya ce babu wani abu da ya wuce tallafin karatu domin babu wata kungiya da za a iya tafiyar da ita bisa jahilci.
