Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zauna da daya daga cikin magabantasa da suka mulki Najeriya, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Rahoto ya zo daga gidan talabiji na Channels cewa tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya zauna da Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Aso Rock.
A wannan zama wanda shi ne na farko tsakaninsu, Jonathan ya yi wa Bola Tinubu bayanin halin da ake ciki a kasar Mali da sauran ƙasashen Nahiyar.

A matsayin shugaban kwamitin sasanci da ECOWAS ta kasashen yammacin Afrika ta tura zuwa Mali, Jonathan ya yi bayanin yadda aka kwana.

Jaridar The Cable ta ce tsohon shugaban na Najeriya ya shaidawa manema labarai cewa ya sa labule da Bola Tinubu ne domin sanar da shi abin da ke faruwa.
