Ƙungiya malaman jami’a a Najeriya ASUU ta bukaci shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sauya tsarin dokar ba da lamuni karatu ga daliban ƙasar.

Shugaban kungiyar na ƙasa Farfesa Emmanuel Osodoke ne ya buƙaci haka a yayin jawabin da ya yi dangane da sanya hannu a kan dokar lamunin karatu da gwamnatin kasar ta yi.

Ya ce a kasashen waje dalibai na kashe kasu saboda bashi da ake binsu bayan lamuntarsu a kan karatun da su ka yi.

A cewar shugaban kungiyar, kyautuwa ya yi a takaita bashi ga dalibai talakawa sa ba su da karfin yin karatun.

Ya kara da cewa, ba lallai ne tsarin da aka yi ya yi tasiri ba duba ga halin da kasar ke ciki.

Sannan ɗalibai da dama ba za su iya biyan bashin ba ko da bayan sun kammala karatun nasu.

Ya ce ko a shekarun baya an yi irin wannan tsarin, sai dai daliban ba sa biyan kudin bayan kammala karatunsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: