Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu ya kai ziyarar ba zata wani babban Asibiti a cikin garin Sokoto domin gane wa idonsa yadda likitoci ke duba marasa lafiya.

Mai magana da yawun gwamnan Jihar Malam Abubakar Bawa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Kakakin gwamnan ya ce gwamna ya kai ziyara ne bayan wasu korafe-korafe da ake yawan kai masa wadanda Al’ummar Jihar ke aike masa dashi akan yadda rashin nagarta yayi yawa a Asibitin.

Bawa ya kara da cewa daga cikin ababuwan da suka sanya gwamna zuwa da kansa Asibitin sun ƙunshi lalacewar mahalli rashin wutar lantarki da lalacewar kayan aikin da na gwaje-gwaje.

Abubakar ya ce gwamna yaje Asibitin ne a babur mai kafa uku wanda aka fi sani da Adaidata Sahu domin ya samu bayanai daga ma’aikatan asibitin da marasa lafiya.

A yayin jawabin gwamnan ya bayyana rashin jindadin akan yadda ya ga asibitin.

Gwamnan ya ce Marasa lafiya da masu jinya na cikin wani hali a mahalli mara kyau ga rashin kayan aikin malaman asibiti.

A ziyarar gwamnan ya zauna da Malayan asibitin domin su lalubo hanyar da za a farfado da kimar asibitin.

Wata majiya daga asibitin ta bayyana cewa tsohuwar hwamnatin Jihar ce ta haifar da lalacewar asibitin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: