Gwamnatin tarayya ta tabbatar da kafa wani kwamiti da zai duba jerin bukatun da kungiyoyin kwadago su ka gabatar.

Jaridar Punch ta bayyana cewa kafa kwamitin na zuwa ne bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur a kasa baki daya.
Gwamnatin ta kafa kwamitin ne a ranar Litinin inda ta bayyana cewa ta kafa wani kwamitin ne domin duba jerin bukatun da kungiyoyin kwadago su ka gabatar mata.

Jaridar ta ce hakan na zuwa ne bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur wanda hakan ya haifar da matsi da wahala ga mutanen Kasa.

Bayan kammala ganawa da kungiyoyin mataimaki na musamman ga shugaban Kasa a fannin sadarwa Dele Alake da shugabannin ma’aikata sun bayyana cewa, shugabannin kungiyoyin NLC da TUC Joe Ajaero da Festus Osifo su ka wakilci ma’aikatan kasar.
A yayin ganawar su da manema labarai sun bayyana cewa an kafa kwamitin da sauran kananun kwamitoci da za su gabatar wa da shugaban bukatun su.
Daga cikin kwamitocin da aka kafa za su gudanar da ayyuka daban-daban.
A yayin jawabin shugaban kungiyar ‘yan kasuwa Festus Osifo ya ce gwamnati ta bada gudumuwarta kuma daga yanzu za su rika yin aiki a tare.
Osifo ya kara da cewa kwamitin zai duba bukatun da aka gabatar kamar samar da motocin haya masu aiki da gas da batun karin albashi.
Joe Ajaero ya ce kwamitocin za su iya kammala zama nan da makonni takwas masu zuwa.