Hukumar raba arzikin kasa (RMAFC) ta musanta rahotannin kafafen yada labarai na cewa ta amince da karin albashin masu rike da mukaman siyasa da na shari’a da na gwamnati da kashi 114 cikin 100.

A wata hira da sukai da jaridar LEADERSHIP, jami’in hulda da jama’a na RMAFC, Christian Nwachukwu, ya ce shugaba Bola Tinubu bai amince da karin albashin ma’aikatan gwamnati ba.


Kwamishiniyar tarayya a hukumar Rakiya Tanko-Ayuba ce ta bayyana karin albashin a lokacin da ta wakilci shugaban RMAFC, Mohammad Shehu, a wajen gabatar da rahoton kasafin kudin da aka duba ga gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, a Birnin Kebbi. ranar Talata.
Tanko-Ayuba ya ce an fara aiwatar da shirye-shiryen biyan kudaden da aka sake dubawa daga ranar 1 ga Janairu, 2023, ikirarin da kakakin hukumar ya musanta.
A cewar sa shugaban su bai taba yin wata magana a kai ba, babu wata magana daga shugaba, babu wata sanarwa daga shi, don haka, bai saniba, ya ji daya daga cikin Kwamishinonin ya ce, ba ya son a ambace shi, Kakakin RMAFC ya shaida wa Wakilin su yayin da yake musanta ikirarin Kwamishinan.
Ya kara da cewa babu amincewa tukuna. Bai san tushen wannan labarin ba. Komai yana ƙarƙashin tsari. Dole ne ya zo a matsayin Bill ga Shugaba don amincewa.
Shugaban kasa bai ba da izini ba. Har sai Shugaban kasa ya ba da izini, ba za ku iya ɗauka kamar an fara aiki ba.
Da aka tambaye shi ko majalisar ta fara aiki kan wannan kudiri, sai ya ce, za a aika da ita ga majalisar dokokin kasar. Ko ta yaya, ko an aika ko ba a aika ba, Shugaban kasa bai amince da shi ba. Dole ne a kammala duk waɗancan tsarin doka, a karshe, za ta sauka a kan teburin shugaban kasa don amincewa. Wannan ba a kammala ba.
Da wakilin jaridar ya tambaya ko hakan na nufin cewa labarin da aka yi kan batun karin albashi ba gaskiya ba ne, Nwachukwu ya ce: Ka dai dauke shi yadda ka fahimce ba gaskiya bane.
Da aka tambaye shi ko RMAFC ta aika da kudirin dokar ta hannun FEC ga Majalisar Dokoki ta kasa don tattaunawa, sai kawai Nwachukwu ya ce: “Komai yana karkashin tsari.”
