Tsohon gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Gunduje ya bayyana cewa baya fargabar ci gaba da binciken fefen bidiyon dala kamar yadda gwamnan jihar ke ikirarin ci gaba da yi a kansa.

Tsohon kwamishinan yada labaran tsohon gwamnan Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan.

Ganduje ya ce dukkan binciken da ake yi akansa ba ya cikin wata fargaba tunda ya san bai aikata abinda ake tuhumarsa da shi ba.

Idan ba a manta ba dai shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano Muhuyi magaji Rimin gado ne ya bayyana ci gaba da bincikar tsohon gwamnan na Kano.

Muhuyi ya kara da cewa bayan batun bidiyon karbar rashawa akwai zarge-zargen da dama da ake yiwa Ganduje ciki harda barnatar da dukiyoyin kananan hukumomin jihar da batun haraji da kuma kwangiloli.

A baya- bayannan ne dai Ganduje ya bukaci da kotu ta haramtawa hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon Kasa ta EFCC kama shi domin gudanar da bincika akansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: