Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya tafi Birnin Landan wata ziyara ta musamman bayan kammala ziyarar aiki da ya kai Kasar Faransa a yau Asabar.

Channels TV ta rawaito cewa hadimi na musamman ga shugaban kan sadarwa da tsare-tsare Dele Alake ne tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Dele ya bayyana cewa shugaban ya kammala ziyarar da ya kai Kasar ta Faransa kuma zai wuce Kasar ta Birtaniya ne daga Kasar ta Faransa.

Dele Alake ya kara da cewa Shugaban zai dawo gida Najeriya kafin ranar idin babbar Sallah.

Kafin bayyana aniyyar shugaban ta tafiya kasar London zai dawo gida Najeriya ne a yau Asabar bayan kammala gudanar da taron da ya halarta a Kasar ta Faransa.
Shugaban yaje kasar ta Faransa ne halartar taron
Bunkasa harkokin Kasuwanci da zuba hannun Jari a nahiyar wanda shugabannin Kasashen Afirka suka tattauna.