Akalla mutane shida ne suka rasa rayukansu bayan wata motar matafiya ta taka wani bin fashewa a cikin Karamar Hukumar Konduga da ke Jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin mayakan Boko Haram da binne bama-bamai akan hanyar wani kauye da ke tsakanin Bama da Kawuri a Karamar Hukumar ta Konduga.
Wani mai fashin baki da akan harkokin tsaro a yankin tafkin Kasar Chadi Zagazola Makama ne ya tabbatar da hakan.

Motar wadda ta taso daga Jihar Adamawa bayan taka bam din mutane biyar da ke cikin motar sun rasa rayukansu.

A yayin harin direban motar ya jikkata daga baya ya rasu bayan ‘yan sa’o’i da fashewar bom din a wani asibiti da ke garin Maiduguri babban birnin Jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa hanyar da ke tsakanin garin Bama da Konduga ta kasance cikin kwanciyar hankali domin ba a samu wani hari ba a cikin shekaru shida da suka gabata.