Wata kotu dake zamanta a Jihar kano ta bayar da umarnin dakatar da hukumar hana cin hanci da rashawa da kuma karbar korafe korafe ta kano PCACC da kuma hukumar tsaron farin kaya ta DSS bisa kama tsohon gwamna Ganduje.

kamar yadda sanarwa ta bayyana daga kotun ta ce a dakata da yunkurin kama Abdullahi Umar Ganduje bisa tuhumar faifan dala.

makon da ya gabata ne shugaban hukumar hana cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar kano Muhuyi magaji Rimin Gado ya tabbatar da ingancin faifan bidiyon da aka hango Ganduje ya na karabar na Goro.

Sai dai kamar yadda aka aikewa gwamnan takardar gayyata, an samu umarni daga kotun jihar na cewa a dakata da wannan kamun da za a yi masa don amsa tambayoyi.

Alkalin kotun Liman ya bayyana cewa an shigar da korafe akan cewa za a muzgunawa gwamnan.

Sai dai alkalin kotun ya ce tun bayan shigar da korafin dole sai an kammala sauraren za a ji matsayar kotu akan gudanar d bincike akan Ganduje.

A shekarar 2018 jaridar Daily ta fitar da wani faifan bidiyo wanda aka hangi tsohon gwamnan jihar kano Abdulahi umar Ganduje ya na karbar na goro daga hannun wasu mutane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: