Akalla mutane 50 ake zargin sun rasa rayukansu a wani mamakon ruwan sama da aka yi kasar Fakistan.

A shafe makonni biyu tun daga ranar 25 ga watan yuni zuwa 8 ga watan Yuly ana gudanar da mamakon ruwan sama a Punjab.
An yi asarar dukiyoyii masu tarin yawa a ruwan da aka yi a yankin na Punjabi.

Dayawa daga cikin rashin ya faru ne daliliin wutar lantarki da kama su da kuma ruftawar gine-gine.

Sannan bayan cikin rashe-rashen da aka yi akwai yara takwas yan kiman shekaru 12 zuwa 15 a yankin Shangala lardin Kaibar.
Sai dai har yanzu ana ci gaba da laliben sauran gawarwakin da ba a gani ba a sauran yankin.