Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta hana gurfanar da dakataccen shugaban hukumar zaɓe INEC reshen jihar Adamawa.

An shirya gurfanar da Hudu Yunusa Ari a gaban kotu bayan ya ayyana Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan jihar.
Mai Shari’a Justice Donatus Okonko ne ya bayar da umarnin hana gurfanar da shi a kotu, baayan wani lauya mai muƙamin SAN ya jagorancin gabatar da korafin.

Lauyoyin sun buƙaci a dakatar daga gurfanar da dakataccen kwamishinan a kotu, har sai kotun sauraron korafin zaɓe ta kammala shari’a.

Jami’an tsaro sun kama Hudu Yunusa Ari bayan an gabatar da korafin a gabansu.
Daga bisani hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta gabatarwa da kotu korafi a kan zaben da ya gudana a jihar Adamawa wanda su ka ce ya ayyana kuskure a zaɓen da ya gudana.
An yi zargin dakatacen kwamishinan da karɓar rashawa domin ayya A’isha Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa.
Kotun ta dakatar da kama ko gurfanar da Hudu Ari tare da ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 18 ga watan Yuli daa mu ke ciki.